Mukala kan Dankwairo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Zamfara a Bakin Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun


Alhaji Ibrahim Muhammad
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin-Magaji (Ɗan Alin Birnin-Magaji), Jihar Zamfara.
08149388452
birninbagaji4040@gmail.com


Tsakure

Arewacin Nijeriya wani yanki ne a ƙasar Hausa da ya haɗa tarin fasihai ta ɓangaren makaɗa da mawaƙa. Mafi yawanci suna gwada hikimarsu cikin harshen Hausa. Da wannan masaniyar aka nemi gwarazan mawaƙa uku (3) waɗanda aka yi ittifaƙin hikimominsu da zalaƙa irin tasu a awon baka, ta yi zarrar da babu mai tababa. Bayan dogon shaƙo wajen nazarin rayuwar mawaƙan baka, an so a ƙara bayani ga ayyukan da magabata suka yi kan Narambaɗa, domin mu taya shanu ciri. An dai fahimci har yanzu akwai buƙatar a ci gaba da nazari a cikin waƙoƙin tsofaffin mawaƙan baka na Hausa, domin a yaba da ƙwazonsu, a kuma amfana da tarin hikimomin da suka naɗe a cikin waƙoƙinsu. Fitilun Kalmomi: Matasa, Ɗanƙwairo, Shata, Narambaɗa.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub